Duniya Na Tir Da Isra’ila Kan Haramta Ayyukan Hukumar (UNRWA)

Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na ci gaba da yin tir da Allah wadai da matakin majalisar dokokin Isra’ila na haramta hukumar kula

Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na ci gaba da yin tir da Allah wadai da matakin majalisar dokokin Isra’ila na haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira na Falasdinu.

Shugaban Hukumar ya ce matakin da majalisar dokokin Isra’ila ta dauka na haramta kungiyarsa yana kara wahalhalun da Falasdinawan ke ciki.

Ministar harkokin wajen Australiya Penny Wong ta ce UNRWA tana aikin ceton rai kuma gwamnatinta na adawa da matakin Knesset na “kayyade” ayyukan hukumar.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce UNRWA ta kasance “hanyar rayuwa da ba za a iya maye gurbinta ba” ga al’ummar Falasdinu shekaru saba’in da suka gabata.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Jordan ta yi Allah-wadai da matakin.

Su ma kasashen Ireland, Norway, Slovenia da Spain duk sun yi tir da haramcin hukumar ta UNRWA daga Isra’ila

Haka zalika su ma gwamnatocin kasashen Turai nan hudu – wadanda dukkansu suka amince da kasar Falasdinu – sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi Allah wadai da matakin na Knesset ga hukumar.

Kasashen hudu sun ce “za su ci gaba da yin aiki tare da masu ba da agaji da kasashen dake tallafawa hukumar don tabbatar da dorewar ayyukanta da rawar da take takawa”.

Kungiyar Hamas ma ta yi Allah wadai da dokar Isra’ilar da ta haramta UNRWA, tana mai cewa ta dauki kudirin a matsayin ” wani bangare na yakin Sahayoniya da cin zarafi ga falasdinawa”.

Jakadan kasar Sin a MDD Ya yi Allah wadai da matakin kuma ya ce akwai bukatar Isra’ila ta sake tunani kan hakan.

Shi ma Jakadan Rasha a MDD, Ya ce wannan matakin da majalisar dokokin Isra’ila ta dauka ya kara dagula al’amura musamman a Gaza. Ya kuma ce wannan mummunan hukunci ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments