Kasar Afirka ta Kudu ta gabatar da takardun dake kunshe kisan kiyashin da Isra’ila ta aikata a Gaza ga kotun kasa da kasa da ke birnin Hague.
A gaban kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya, Pretoria ta zargi gwamnatin Sahyoniya da karya yarjejeniyar kisan kare dangi a Gaza.
A farkon shekarar 2024, alkalan kotun sun yi la’akari da cewa akwai yuwuwar yin kisan kare dangi inda suka umarci Isra’ila da ta ba da damar shigar da kayan agaji a yankin.
Matakin na Afrika ta Kudu tamakar wani babi ‘’daya’’ a cikin shari’ar da ake sa ran za ta dauki shekaru da yawa.
Pretoria ta gabatar da takaitaccen bayani mai shafuka 750, mai kwararan hujjoji.
Afirka ta Kudu ta kuma bukaci a tsagaita wuta a Lebanon da Falasdinu.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya jaddada cewa matakin da Pretoria ta dauka a gaban kotun yana da nufin “tabbatar da hadin kan duniya daya taimaka wa Afirka ta Kudu ficewa daga mulkin wariyar launin fata”.