A wata tattaunawa ta wayar tarho, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a yankin tare da jaddada muhimmancin hana ayyukan da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin.
A cikin wannan tattaunawa ta wayar tarho, bangarorin biyu sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da sabbin ci gaban da ake samu a yankin, da kuma sakamakon karuwar tashe-tashen hankula.
Ministocin harkokin wajen Iran da na Saudiyya sun jaddada muhimmancin kauracewa ayyukan da ke kawo barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin.