Masar Ta Gabatar Da Bukatar Tsagaita Ta Kwanaki Biyu A Gaza

Shugaban Masar Abdel Fattah al Sissi ya bayyana cewa, kasar ta ba da shawarar tsagaita bude wuta na kwanaki biyu a zirin Gaza wanda zai

Shugaban Masar Abdel Fattah al Sissi ya bayyana cewa, kasar ta ba da shawarar tsagaita bude wuta na kwanaki biyu a zirin Gaza wanda zai kunshi musayar fursunonin Isra’ila hudu da aka yi garkuwa da su.

Al Sissi wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a birnin Alkahira ya kara da cewa, za a ci gaba da tattaunawa da nufin cimma matsaya ta dindindin a cikin kwanaki 10 da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi.

Bayanai sun ce tuni aka tattauna, tsakanin manyan jami’an  leken asiri na Masar da Isra’ila da kuma na wasu kasashen yankin da na kasa da kasa.

To saidai rahotanni daga baya bayan sun ce Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shirin da Masar ta gabatar na tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza da aka yi wa kawanya.

Duk da goyon bayan da akasarin ministocin Isra’ila suka yi kan shawarar Masar, Tel Aviv ta yanke shawarar yin watsi da yarjejeniyar ne saboda adawar Netanyahu, wanda ya jaddada cewa “za a yi tattaunawar ne kawai ana cikin yakin,” a cewar tashar 12 ta Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments