Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Ce Babu Makawa Iran Za Ta Mayar Da Martani Kan Isra’ila

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Babu makawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga zaluncin yahudawan sahayoniyya Shugaban

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Babu makawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga zaluncin yahudawan sahayoniyya

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Babu makawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya, yana mai cewa sashi na 51 na kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya ya bai wa Iran damar kare kanta daga duk wani matakin wuce gona da iri.

Qalibaf ya bayyana hakan ne a farkon zaman taron Majalisar Shwarar Musulunci a yau Lahadi cewa: Nasara da jihadin wadanda suka sadaukar da kansu a fagen tsaron sararin samaniyar Iran na sojoji da dakarun kare juyin juya halin Musulunci yana nuna cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kasance abin yi wa dariya a ko da yaushe a duniya idan suka fuskanci al’ummar Iran masu girma da daraja a kowane yaki.

Shugaban Majalisar ya kara da cewa: Kwatanta tsakanin harin daukan fansa na Alkawarin Gaskiya na 2 da kuma matakin soji na baya-bayan nan na yahudawan sahayoniyya, shaida ne a fili kan irin karfin mayar da martanin da sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke da shi, kuma gwamnatin yahudawan sahayoniyya babu wata nasara da ta samu face kisan kiyashi da kuma kashe mata da yara marasa tsaro a Gaza da Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments