Rundunar sojin Iran na kara fitar da bayani game da harin da Isra’ila ta kai wa kasar a cikin daren ranar Asabar.
A sanarwar data fitar rundinar ta ce, Isra’ila ta yi amfani da sararin samaniyar kasar Iraki da ke karkashin ikon Amurka wajen kai hari kan Iran.
Rundinar ta kara da cewa dakarun sojin Iran sun yi nasarar hana jiragen yakin Isra’ila shiga sararin samaniyar kasar.
Sanarwar ta kara da cewa na’urorin radar kan iyaka a lardin Ilam da Khuzestan (yammacin kasar Iran) da kuma kewayen lardin Teheran,” sun dakile hare-haren makamai masu linzami da aka harba a nisan kilomita 100 daga sararin samaniyar Iran.
A cewar sanarwar wani rukunin na na’urorin radar na Iran sun sami ‘yar barna da ba ta da tasiri” sakamakon harin da Isra’ila ta kai musu.
Tun da farko dai rundunar sojin kasar Iran a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar ta ce Isra’ila, ta kaddamar da hare-hare kan wasu wuraren soji a lardunan Tehran, Khuzestan da Ilam, inda ta kara da cewa ana gudanar da bincike.