Sojojin Isra’ila Sun Kashe Falasdinawa 45 A Wani Samame Kan Gaza

Bayanai daga Falasdinu na cewa sojojin Isra’ila sun kai wani mummunan hari da bama-bamai kan wasu gine-gine shida a birnin Beit Lahia da ke arewacin

Bayanai daga Falasdinu na cewa sojojin Isra’ila sun kai wani mummunan hari da bama-bamai kan wasu gine-gine shida a birnin Beit Lahia da ke arewacin zirin Gaza, inda suka kashe mutane akalla 45.

An kuma jikkata wasu da dama bayan harin da aka kai kan gine-ginenb a ranar Asabar.

Hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da tsananin hare-haren sojojin na Isra’ila ya tilastawa hukumar tsaron farar hula ta Falasdinu dakatar da ayyukanta a yankin.

Da yake tsokaci game da halin da ake ciki, Darakta Janar na Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, Medhat Abbas, ya ce sama da Falasdinawa 900 ne aka kashe a cikin makonnin da suka gabata a yakin da Isra’ila ke yi kan yankunan arewacin Zirin.

Ya kara da cewa Asibitin Kamal Adwan, asibiti na karshe da ke aiki a arewa, na cikin tsaka mai wuya, wanda ko dai an kashe dukkan likitocin asibitin ko kuma an tilasta musu gudu, in ban da likitoci uku da suka rage a can.

Abbas ya ce, “’yan Mamayar sun aikata kisan kiyashi ta hanyar lalata tsarin kiwon lafiya a Gaza.”

Adadin dai Falasdinawa da sukayi shahada tunsoma farmakin na Isra’ila kan zirin ya zarce dubu 42 da 924, galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu 100,833.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments