Jami’ar Milan a Italiya ta yanke alakarta da wata jami’ar Isra’ila

Sakamakon matsin lamba na dalibai da malaman jami’a, Jami’ar Milan da ke Italiya ta kawo karshen hadin gwiwa da wata jami’a ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Sakamakon matsin lamba na dalibai da malaman jami’a, Jami’ar Milan da ke Italiya ta kawo karshen hadin gwiwa da wata jami’a ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Jami’ar Milan ta Italiya, wacce take a matsayin  daya daga cikin manyan jami’o’i a Turai, ta yanke hadin gwiwarta da jami’a mai zaman kanta a haramtacciyar kasar Isra’ila sakamakon matsin lambar dalibai da malaman jami’ar.

Rahotannin sun ce Jami’ar Jihar Milan ko kuma (UNIMI) da ke arewacin kasar ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyoyin hadin gwiwar kimiyya da jami’ar Reichman da ke birnin Herzliya da ke arewacin lardin Tel Aviv da ke Falastinu da yahudawa suka mamaye.`

A gefe guda kuma, jaridar Italiya ta bayar da wani rahoto  inda ta nakalto cewa, kungiyar matasan Falasdinawa da kungiyar dalibai sun taka rawa wajen matsa lamba kan matakin da jami’ar Milan ta dauka na dakatar da hadin gwiwa da jami’ar ta Isra’ila.

Hakan dai na faruwa ne bayan ‘yan watannin da jami’ar Milan ta yanke huldar ta da jami’ar Ariel ta Isra’ila da ke a wani matsugunin yahudawa ‘yan share wuri zauna a tsakiyar gabar yammacin kogin Jordan.

Daliban Jami’ar Jihar Milan a bazarar da ta gabata sun nuna rashin amincewarsu da hadin gwiwar da ke tsakanin jami’ar da kuma  jami’o’in gwamnatin sahyoniyawan bayan hare-haren soji da kisan kiyashin da Isra’ila ta kaddamar a kan al’ummar yankin zirin Gaza, wanda ya zuwa yanzu yayi sanadin shahadar sama da mutane  dubu 42 da 800, tare da jikkatar 100,300, akasarinsu mata da kananan yara, yayin da kuma sama da 10,000 suka bace, a karkashin barazaguzai na gine-ginen da Isra’ila ta rusa a Gaza.

 A yayin  zanga-zangar da  daliban jami’ar Milan  suka gudanar sun kafa babbar tutar Falasdinu a kan ginin tarihi na wannan jami’a tare da kafa tanti a harabar jami’a.

Sun jaddada wajabcin hana sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila kai hare-hare a birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza, tare da zargin gwamnatin kasarsu da hada baki da Isra’ila a kisan gillar da ake yi a Gaza.

Jami’o’in Bologna, Federico II da Spinza da ke Rome su ma sun shaida zama dalibai domin nuna goyon baya ga  Falasdinu a watannin da suka gabata. Masu zanga-zangar sun kuma bukaci dakatar da hadin gwiwar  tsakanin jami’oin su  da Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments