Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Isra’ila, Ta Kuma Tabbatar Da ‘Yancinta Na Kare Kai

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila suka kai kan wasu wuraren soji a kasar,

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila suka kai kan wasu wuraren soji a kasar, tare da bayyana hakan a matsayin keta dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin MDD.

Ma’aikatar ta jaddada cewa wadannan ayyuka na nuni da yin barazana kai tsaye ga ‘yancin kan kasar Iran.

Sanarwar ta yi nuni da hakkin kare kai da Iran ke da shi, kamar yadda aka zayyana a shafi na 51 na Yarjejeniya Ta Duniya.

Iran ta ci gaba da cewa tana da hujja kuma wajibi ne ta kare kanta daga wuce gona da iri.

Gwamnatin Iran ta nanata kudurinta na amfani da duk wani abu da ake da shi don kare tsaronta.

Iran ta kuma nuna godiya ga kasashen da suka yi Allah wadai da wannan ta’addancin da Isra’ila ke yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments