A jiya juma’a Falasdinawa 60 su ke yi shahada a yankunan “Manara” da Qizan-al-najjar dake garin Khan Yunus a kudancin Gaza.
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa; ‘Yan mamaya sun tafka kisan kiyashi ta hanyar kai wa mutane hare-hare a gidajensu.
A tashin farko an kai shahidai 38 zuwa asibitocin yanki, da wasu masu yawa da su ka jikkata, mafi yawancinsu mata da kananan yara.
Sojojin mamayar sun kuma harba manyan bindigogi a yankin arewaci da gabashin garin Rafah.
Daga fara yakin Gaza zuwa yanzu,adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da kuma jikkata sun kai 142,000 kuma wasu da adadinsu ya kai 10,000 sun bace.
Sojojin mamayar HKI sun kuma rusa gidaje da lalata duk wani abu mai muhimmanci na rayuwa a fadin Gaza.
Bugu da kari, ‘yan mamayar HKI sun jefa yankin Arewacin Gaza cikin yunwa, tare da hana shigar da duk wani kayan abinci da agaji.
Wasu Falasdinawan 25 sun yi shahada a harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai akan gidajen mutane a Beit Lahiya dake arewacin Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rusa gidajen fararen hula 11.
Asibitocin yankin suna fama da karancin kayan aiki da magani, bayan da ‘yan mamaya suka hana a shigar da shi daga waje.