Mataimakin Shugaban Iran Ya Yi Fatali Da Da’awar Hahaddiyar Kasashen Larabawa Kan Tsibiran Iran  

Mataimakin shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Tsibirai uku da suke mallaki Iran ba zasu taba zama mallakin wata kasar Larabawa take da’awar cewa mallakinta

Mataimakin shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Tsibirai uku da suke mallaki Iran ba zasu taba zama mallakin wata kasar Larabawa take da’awar cewa mallakinta ne ba

Mataimakin shugaban kasar Iran Muhammad Reza Arif ya ce: Kowa ya san cewa tsibiran guda uku da wasu suke da’awar cewa tasu ce, tsibirai ne na Iran ne, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da tabbatar da cewa mallakinta ne dangane da wannan batu.

A gefen taron tunawa da shahidi Abbas Nilfroshan dangane da da’awar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa take yi na mallakar tsibiran Iran guda uku, Arif ya bayyana cewa, kowa ya san cewa tsibiran guda uku na Iran ne, kuma ba za mu yi sakaci ba ta kowace fuska dangane da wannan batu.

A nashi bangaren, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei a baya ya yi kakkausar suka kan maimaita zarge-zarge marasa tushe dangane da tsibiran Iran guda uku da ke gabar tekun Farisa, a cikin bayanin karshe na zaman taron hadin gwiwa na shugabannin kungiyar Tarayyar Turai da na kungiyar hadin gwiwar kasashen Larabawan yankin Tekun Farisa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments