Qalibaf : Ya kamata kasashen musulmi su kakaba wa Isra’ila Isra’ila ta kunkumi

Kakakin majalisar dokokin Iran ya bukaci kasashen musulmi da su hada gwiwa domin daukar matakan kakaba wa Haramtacciyar Kasar Isra’ila takunkumin tattalin arziki da kuma

Kakakin majalisar dokokin Iran ya bukaci kasashen musulmi da su hada gwiwa domin daukar matakan kakaba wa Haramtacciyar Kasar Isra’ila takunkumin tattalin arziki da kuma katse muhimman hanyoyin rayuwa ga haramtacciyar gwamnatin ‘yan ta’addan sahyuniya.

Yayin wani taro da jakadun kasashen musulmi day a gudana a wanann Talata a birnin Tehran, Mohammad Baqer Qalibaf ya bukaci kasashen musulmi da su yi amfani da “hanyoyin kasa da kasa” don yin Allah wadai da laifukan Isra’ila.

“Ya kamata kasashen musulmi su yi aiki tare da hadin gwiwa don yin amfani da hanyoyin kasa da kasa wajen yin Allah wadai da laifukan gwamnatin Sahayoniya tare da tabbatar da tsagaita bude wuta.”

Qalibaf ya jaddada rawar da jakadun ke takawa, inda ya bayyana cewa za su iya yin kira ga gwamnatocinsu da su ba da goyon baya ga al’ummar Gaza da Lebanon da ake zalunta.

Kakakin majalisar dokokin Iran ya ce “A wannan mawuyacin lokaci, al’ummar musulmi suna da wani gagarumin nauyi a wuyansu na mayar da martani kan laifukan yakin Isra’ila a kan musulmi.”

Qalibaf ya kuma yi tsokaci kan ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila a yankin. “Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta jefa yankin cikin zubar da jini da hargitsi. Wannan gungun masu aikata laifuka da taimakon wasu kasashe, suna tada tarzoma da nufin sauya yanayin siyasar yankin gabas ta tsakiya.

Ya yi gargadi kan yin shiru, da nuna rashin damuwa game da laifuffukan Isra’ila, domin hakan shi ne babban abin da yake kara karfafa gwiwearsu wajen aikata laifukan yaki, da kuma goyon bayan da suke samu kai tsaye daga Amurka wajen aikata hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments