Shugabanin Kasashe Mambobin BRICS Na Isa Rasha Domin Halartar taron Kungiyar Karo Na 16

Shugabannnin kasashe mambobin BRICS, na isa kasar Rasha domin halartar taron kungiyar karo na 16 a binrin Kazan. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya isa

Shugabannnin kasashe mambobin BRICS, na isa kasar Rasha domin halartar taron kungiyar karo na 16 a binrin Kazan.

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya isa birnin na Kazan na kasar domin halartar taron.

A ranar Laraba ne shugaba Pezeshkian zai gabatar da jawabi a babban taron kasashen BRICS, wanda zai hada shugabannin kasashe mambobin BRICS.

Baya ga Pezeshkian, shugabannin kasashen Rasha, China, Afirka ta Kudu, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Fira Ministan Indiya za su halarci taron.

Ministan harkokin wajen Brazil kuma zai halarci taron, wanda zai wakilci shugaban kasar Brazil, wanda ba ya nan saboda rashin lafiya.

A ranar Alhamis, an tsara shugaban kasar Iran zai halarci taron kasashen BRICS Plus, wanda ya hada da kasashe masu sha’awar yin hadin gwiwa da kawancen BRICS, karkashin tutar “BRICS da Global South.”

Mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin siyasa na fadar shugaban kasar ya bayyana cewa, shugaba Pezeshkian zai gabatar da jawabai uku a taruka daban-daban na BRICS, tare da yin shawarwari tsakanin shugabannin kasashen Rasha, Sin, Indiya, Masar, da sauran kasashen duniya, domin kulla alaka.

An bayyana cewa tawagogi daga kasashe 36 zasu halarci taron kungiyar kasashen ta BRICS da arzikinsu ke bunkasa.

Akwai yiwuwar kasashen su kulla yarjejeniya kan sabon tsarin hada-hadar kudi tsakaninsu wadanda babu ruwansu da dalar Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments