Hezbollah Ta Dauki Alhakin Kai Harin jirgi Maras Matuki Kan gidan Netanyahu

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta ce ita ce ta kai harin jirgi maras matuki kan gidan shakatawa na firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a makon

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta ce ita ce ta kai harin jirgi maras matuki kan gidan shakatawa na firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a makon da ya gabata, kamar yadda jami’in hulda da yada labarai na Hizbullah Muhammad Afif, Mohammed Afif ya bayyana.

Jami’in ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar aDahiyeh na Beirut, Afif ya jaddada cewa mayakan Islama zasu ci gaba da fatattakar Netanyahu, dare da rana.

Afif ya yi nuni da cewa, hasarar da makiya suka yi, dangane da sojoji da tankokin yaki na da yawa, musamman a arangamar Aita Al-Shaab.

Afif ya kara da cewa, har yanzu kungiyar Hizbullah na ci gaba da kai hare-hare kan barikokin sojin Isra’ila da sansanoninsu, yayin da makiya ke mayar da martani ta hanyar kai wa fararen hula hari.

A makon da ya gabata ne dai wani harin jirgi maras matuki ya rusa wani bangare na gidan shakatawar Benjamin Netanyahu duk da cewa babu wani da ya samu rauni.

A lokacin Benjamin Netanyahu ya dora alhakin harin kan Hezbollah, a shafinsa na X.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments