Kungiyar Jihadul-Islami Ta Karyata Kashe Babban Sakatarenta Da Wasu Kafafen Yada Labarai Ke Watsawa

Kungiyar Jihadul- Islami ta musanta kashe babban sakatarenta Ziyad al-Nakhalah a kasar Siriya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Jihadul-Islami ta Falastinu ta yi kakkausar suka tare

Kungiyar Jihadul- Islami ta musanta kashe babban sakatarenta Ziyad al-Nakhalah a kasar Siriya

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Jihadul-Islami ta Falastinu ta yi kakkausar suka tare da musanta abin da wasu kafafen yada labaran makiya suka ruwaito game da kishe babban sakatarenta, Ziyad al-Nakhalah ta hanyar kai hari kan wata motar farar hula a birnin Damascus a yammacin jiya Litinin.

A nassin bayanin da kungiyar ta Jihadul-Islami ta Falasdinu ta fitar ta yi kakkausar suka a dunkule da kuma filla-filla kan abin da wasu kafafen yada labarai na makiya suka ruwaito game da aiwatar da kisan gilla kan babban sakatarenta dan gwagwarmaya kuma kwamandan ‘yan gwagwarmaya Ziyad al-Nakhalah, {Allah ya kare shi} a wani hari da aka kai kan wata mota a birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya a wannan Litinin din da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments