Kungiyar Hizbullah Ta Harbo Jirgin HKI Samfurin “Hermes 900”

A sanarwar da dakarun Hizbullah su ka fitar sun bayyana cewa da marecen jiya Lahadi sun kai hare-hare har sau 9, daga ciki har da

A sanarwar da dakarun Hizbullah su ka fitar sun bayyana cewa da marecen jiya Lahadi sun kai hare-hare har sau 9, daga ciki har da kakkabo jirgin sama maras matuki samfurin “Hermes 900”.

Bugu da kari sanarwar dakarun kungiyar ta Hizbullah ta kunshi cewa sun kai wasu hare-hare akan inda aka girke manyan bindigogin da sojojin na HKI suke kai wa Lebanon hari da su.

Da safiyar yau kuwa, mayakan na Hizbullah sun kai wasu hare-haren a sassa mabanbanta na sojojin mamaya da su ka fara tun daga karfe 8: 15, na sifiya kuma suke cigaba har yanzu.

Sojojin na mamaya da su ka yi kutse a gefen garin markaba, sun fuskanci hare-hare da makamai masu linzami daga mayakan na gwagwarmaya. Bayan da aka jikkata wasu daga cikinsu, su ma sojojin da su ka zo daukarsu sun fuskanci wani sabon hari daga kusa da bindigogi.

Wani yankin da ‘yan gwagwarmayar su ka kai wa hari shi ne mahadar garin Udaisa da Rub Salasin da misalin karfe 1:30 na ranar yau ta hanyar harbawa sojojin mamaya da suke son yin kutse makamai masu linzami.

Rahotanni da suke fitowa daga HKI sun ce, an kai wadanda su ka jikkata su 15 zuwa asibitin Zif dake garin Safad.

A gefe daya mayakan kungiyar Hizbullah sun harba makamai masu linzami zuwa garin Haifa, wanda shi ne birni na biyu a HKI bayan birnin Tel Aviv.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments