Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baghaei ya yi kakkausar suka kan ci gaba da aikata munanan laifukan yaki da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa a kan al’ummar Palastinu, wadanda a cewarsa yahudawan sahuyiniya suna ci gaba da aiwatar da su sakamakon gazawar kasashen duniya.
Baghaei ya ce, “Abin kunya ne a ce gwamnatin Isra’ila a kullum tana aikata laifuka iri-iri da ayyukan ta’addanci a kan al’ummar Palasdinu sakamakon shiru da rashin daukar matakin sauke nauyi daga kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama.”
Ya kara da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da aikata laifukan da take aikatawa kan Falasdinawa saboda rashin hukunta ta, da kuma goyon bayan da take samu kai tsaye daga Amurka kan dukaknin laifukan da take aikatawa.
Kakakin ya kara da cewa, kisan gillar da aka yi wa Falasdinawa da dama a birnin Beit Lahia da ke arewacin Gaza da kuma farmakin da daruruwan yahudawan sahyoniya masu tsatsauran ra’ayi suka kai a harabar masallacin Al-Aqsa, na nuni ne da wani shiri mai hadari da gwamnatin sahyoniyawa take da shi, da nufin kawar da duk wata alama ta al’ummar Palasdinu da wurare masu tsarki na al’ummar musulmi da ke cikin Falastinu.
Baghaei ya yi gargadi game da mummunan sakamako maras tabbas na ci gaba da aikata laifuka da cin zarafi da Isra’ila ke yi kan al’ummar Palasdinu.
Ya yi kira ga al’ummomin duniya da gwamnatocin Musulunci da su gaggauta mayar da martani game da laifuffukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take aikatawa tare da hukunta “shugabanninta masu laifi”.
Har ila yau jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada cewa, kasarsa tana nan kan bakanta wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na na Musulunci da kuma ‘yan adamtaka wajen ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinu.