Matasa a kasar Iraki sun kai hari kan ofishin tashar talabijin ta MBC ta Saudiyya da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar tare da kona ta
Hotunan faifan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wasu fusatattun mutane suka kutsa kai cikin ofishin tashar Saudiyya ta MBC da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki a jiya Asabar, inda suka farfasa kayan aikin tashar talabijin din tare da cinna wuta ga ginin sakamakon wani rahoto na batanci ga shugabannin Falasdinu, Iraki, da kuma ‘yan gwagwarmayar Lebanon, tana mai bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.
Jami’an tsaron Iraki sun rufe hanyoyin da ke kan hanyar zuwa helkwatar tashar da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar.
A cikin wani rahoto mai cike da cece-kuce mai taken “Millennium of Freedom from Terrorism” tashar MBC ta Saudiyya ta bayyana sunayen jagororin kungiyoyin gwagwarmayar wadanda suka yi shahada da rayayyu, ciki har da kwamanda Hajj Qassem Soleimani, Sayyed Hassan Nasrallah, Imad Mughniyeh, Jihad Mughniyeh, Samir Quntar, Fouad Shukr da Sayyed Badar al-Din al-Houthi da Abu Mahdi Al-Muhandis da Isma’il Haniyyah da Yahya Al-Sinwar, sai ta zarge su da ta’addanci. Tashar talabijin ta Saudiyya ta bayyana shahidi Qassem Soleimani, kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, wanda ya taka gagarumar rawa wajen dakile ayyukan ta’addanci kungiyar ta’addanci ta ISIS, a matsayin alamar ta’addanci kuma sanadin yaki da barna, sannan ta kara da cewa: Ya gudanar da ayyukan banza da suka ƙare a shekara ta 2020.