Hezbollah: Mun shiga sabon matakin tsananta ayyukan soji a kan Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da fara wani sabon mataki na daukar fansa kan kasar Isra’ila, wadda ta shafe sama da shekara

Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da fara wani sabon mataki na daukar fansa kan kasar Isra’ila, wadda ta shafe sama da shekara guda tana kai hare-hare kan Lebanon da Gaza.

A cikin wata sanarwa da aka fitar da sanyin safiyar Juma’a, ofishin gudanarwa na kungiyar Hizbullah ya sanar da “canza wani sabon mataki a cikin arangama da makiya yahudawan Sahyunia.”

A cewar sanarwar, an yanke hukuncin ne “bisa ga umarnin shugabancin koli na Rundunar mayakan ta Hizbullah.”

Da take ba da cikakkun bayanai game da ci gaba da tinkarar dakarun Isra’ila, kungiyar ta ce arangama tsakanin mayakan Hizbullah da dakarun mamaya ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Isra’ila 10 tare da jikkata wasu sama da 150, da kuma tankokin yaki na Merkava 9 da kuma bisldoza na soji hudu a farkon makon nan.

Hezbollah ta kara da cewa ta yi amfani da makamai masu linzami da ake sarrafawa a karon farko a yakinta da Isra’ila.

Ta kara da cewa ta yi amfani da jirage marasa matuka daban-daban, ciki har da na zamani da aka tura a karon farko, a hare-haren da ta kai kan sansanonin sojin Isra’ila.

A cewar sanarwar, jirage marasa matuka na kungiyar sun kuma gudanar da ayyukan leken asiri.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, mayakan da ke cikin sashen tsaron sama na kungiyar sun harbo jiragen leken asiri guda biyu na Isra’ila, Sanann kuma tun daga ranar da sojojin Isra’ila suka kutsa kai cikin Lebanon sama da makonni biyu da suka gabata ya zuwa yanzu, mayakan Hizbullah sun halaka sojojin Isra’ila 5 da kuma jikkata wasu da dama, tare da tarwatsa tankokin Mirkava 23 da kuam buldoza 4 da motocin daukar sojoji 2, in ji sanarwar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments