Dubban Mutane Ne Suka Halarci Jana’izar Shaida Abbas Nilforoushan A Birnin Esfahan Na Kasar Iran

Dubban daruruwan mutanen birnin Esfahan na kasar Iran sun yi rakiyar Jana’izar shahid Burgedia Janar Abbas Nilforoushan wani babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin

Dubban daruruwan mutanen birnin Esfahan na kasar Iran sun yi rakiyar Jana’izar shahid Burgedia Janar Abbas Nilforoushan wani babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci ko IRGC, inda aka kwantar da shi a makabartar Golzor Shuhada ta Esfahan.

Kamfanin dillacin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa masu rakiyar gawar Nilforoushan su na sanye da bakaken kaya, sannan suna dauke da akwatin gawarsa lullube da tutar Iran suna wucewa ta tsakiyar birnin, suna rera shi’arai na All..ya kashe HKI All..ya kashe Amurka.

Shahid Nilforoushan ya yi shahada a ranar 27 ga watan satoban da ya gabata a lokacin da jiragen yakin HKI suka yi ruwan boma boman har ton 80 kansa da kuma kan shugaban kungiyar Hizbullah na  kasar Lebanin Shahid Sayyid Hassan Nasarallah a unguwar dahiya junubiyya na birnin Beirut.

Labarin ya kara da cewa bayan gano gawarsa a karkashin ginegin da aka rusa a kansu, an kai shi birane Karbala da Najaf na kasar Iraki sannan aka zo dashi nan Tehran da kuma birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar Iran kafin a kaishi makwancinsa na karshe a birnin Esfahan a jiya Alhamis. Burgediya Janar Abbas Nilforoushan dai mai bada shawara ne na IRGC a cikin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments