Mahukuntan Burtaniya sun hana jikan Mandela shiga kasar saboda goyon bayan Gaza

Kungiyar gwagwarmayar hadin kan Falasdinu ta Scotland (SPSC) ta shirya jerin tattaunawa a makon da ya gabata tare da Mandla Mandela, jikan tsohon shugaban kasar

Kungiyar gwagwarmayar hadin kan Falasdinu ta Scotland (SPSC) ta shirya jerin tattaunawa a makon da ya gabata tare da Mandla Mandela, jikan tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu wanda ya yi yaki da wariyar launin fata.

Tattaunawar ta gudana a Edinburgh, Dundee, Aberdeen, da Glasgow, da kuma a birane hudu na Ingila da Dublin, Ireland.

Sai dai duk da cewa a baya Mandela ya rike takardar izinin shiga  Burtaniya ta tsawon shekaru, amma ya fuskanci tsaiko wajen bayar da bizarsa, lamarin da ya hana shi tafiya Birtaniya.

Kungiyar ta SPSC ta bayyana damuwarta kan cewa da gangan ne gwamnatin Birtaniya ta jinkirta bizar Mandela saboda tsananin adawa da yake yi da zaluncin “Isra’ila” da kuma goyon bayansa ga karar da gwamnatin Afirka ta Kudu ta kai Isra’ila a gaban kotun kasa da kasa (ICJ).

A watan Janairu, Afirka ta Kudu ta shigar da kara a gaban kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya, inda ta zargi “Isra’ila” da aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza tare da neman kotun ta umurci sojojin Isra’ila da su daina kai hare-hare.

Kotun ta ICJ ta ce dole ne Isra’ila ta dauki dukkan matakan da suka dace don hana kisan kare dangi a Gaza, duk da cewa kotun  ba ta bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa ba.

Gwamnatin Burtaniya ta musanta cewa an toshe takardar iznin Mandela ne saboda goyon bayansa ga wannan shari’ar, inda ta bayyana wa SPSC cewa jinkirin yana da alaka ne da wasu tsare-tsare kawai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments