Iran Ta Bukaci Kungiyar Shanghai Ta Tsaya Kan Goyin Bayan Falasdinawa Da Kuma Yin Tir Da HKI

A taron Jami’an gwamnatocin kungiyar ‘Shanghai Cooperation Organization (SCO)’ da ke gudana a birnin Islamabad na kasar Pakistan, kasar Iran ta bukaci kasashen kungiyar su

A taron Jami’an gwamnatocin kungiyar ‘Shanghai Cooperation Organization (SCO)’ da ke gudana a birnin Islamabad na kasar Pakistan, kasar Iran ta bukaci kasashen kungiyar su fito fili su yi tir da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a kasar Falasdinu, su kuma hada kai don yin hakan.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce, gwamnatin Iran ta bukaci kasashen kungiyar ta (SCO) su dauki matakai bai daya kuma a aikace kan HKI kamai takaita ko kuma katse huldar kasuwanci da HKI, daga ciki har da akuracewa kayakin da ake yinsu a haramtacciyar kasar.

Muhammad Atabak ministan masana’antu, ma’adinai da kasuwanci na kasar Iran, sannan shugaban tawagar kasar zuwa taron na birnin Islamabad ya gudewa gwamnatin kasar Pakistan kan daukan nauyin taron, ya kuma yi maraba da kasar Belerus a matsayin sabon mamba a kungiyar sannan ya taya kasar Rasha murnar karbar shugabancin majalisar firai ministoci na kungiyar.

A wani sashe na maganarsa Atabak ya yi tir da kissan kiyashen da HKI take yi a kasashen Asiya ta kudu, ya kuma kasashen kungiyar suyi aiki tare don ganin an dawo da doka da oda a duniya, da kuma mutunta al-amuran cikin gida da ya shafi ko wace kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments