Iran Kasashe Da Rayuwa Tare Da Mabiya Addinai Daban-Daban

Mabiya addinin kirista a nan Iran suna rayuwa tare da sauran Mabiya addinai daban daban. Pasto Ninus Mukaddas niyo na cocin Angika a nan Iran

Mabiya addinin kirista a nan Iran suna rayuwa tare da sauran Mabiya addinai daban daban.

Pasto Ninus Mukaddas niyo na cocin Angika a nan Iran ya bayyana cewa kiristoci a Iran suna rayuwa tare da sauran Mabiya addinai daban daban a kasar cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Kamfanin dillancin  labaran Parstoday ya nakalto Ninus Mukaddas niyo yana a ganawarsa da hukumar al-adu da sada zumunci na addinin musulunci a nan Tehran.

Ninus Mukaddas niyo ya kara da cewa akwai wata tawagar kiristoci suka suka zirici JMI daga kasashen da dama suka kuma ga yadda kiristoci a nan kasar suke zaman lafiya tare da sauran Mabiya addinai daban daban. Inda suka ziyarci birane da garuruiwa da dama don ganewa idanunsu yadda kiristoci suka rayuw a kasar Iran.

Paston ya kara da cewa wasu da dama sun fito daga kasashen da basa ga maciji da kasar Iran, kuma ya tabbatar da cewa zasu isar da sakonni masu muhimmanci ga kiristoci a kasashen su.

Yace kasashen yamma da dama suna farfaganda wacce ba gaskiya ba dangane da JMI da kuma sauran addinin. Kuma ya tabbatar da cewa an fi mutunta addini a kasar Iran fiye da wasu kasashen yamma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments