Hizbullah : Isra’ila Barazana Ce Ga Daukacin Yankin­_ Qassem

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya yi gargadin cewa mamayar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa Falasdinu barazana ce ba ga Falasdinu kadai ba, har

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya yi gargadin cewa mamayar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa Falasdinu barazana ce ba ga Falasdinu kadai ba, har ma ga daukacin yankin da ma sauran yankunan.

Sheik Naim Qassem ya bayyana haka a jawabinsa na uku da ya yi ta gidan talabijin tun bayan shahadar shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah,

Sheik Qassem ya ce “Isra’ila ‘yar mamaya ce, kuma hadari ce ga daukacin yankin da ma duniya baki daya.”

Ya ce Isra’ila kuma tana da burin mamaye yankunan kasashen Larabawa da na musulmi.”

Jami’in na Hizbullah ya jaddada muhimmancin tsayin daka wajen tinkarar kisan kiyashin da Isra’ila da masu mara mata baya suke yi.

“Isra’ila da wadanda ke bayanta suna mana kisan kiyashi, ba abin da ya rage mana illa mu tashi tsaye.”

Jami’in na Hizbullah ya kuma fallasa shirin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila a yammacin Asiya. Na samar da abun da suke kira sabuwar Gabas ta Tsakiya.

Jami’in na Hizbullah ya ce idan har Tel Aviv na son ‘yan sahayoniyawan su koma gidajensu a yankunan arewacin kasar da ta mamaye, to dole ne ta dakatar da hare-haren da take kaiwa Gaza da Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments