Iran Ta Nuna Bacin Rai, Game Da Sabbin Takunkuman EU

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi jakadan kasar Hungary da ke birnin Tehran domin isar masa da gagarumar bacin ran kasar da kuma nuna

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi jakadan kasar Hungary da ke birnin Tehran domin isar masa da gagarumar bacin ran kasar da kuma nuna adawa da sabon takunkumin da kungiyar tarayyar turai ta kakabawa wasu daidaikun mutane da hukumomin Iran.

A ranar litni ne kungiyar ta EU ta amince da sabbin takunkumai kan wasu mutane 7 na Iran da wasu hukumomi 7 da suka hada da kamfanin jirgin saman kasar Iran Air, bisa zargin mikawa Rasha makamai masu linzami domin yakin Ukraine.

Jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi tir da matakin “wanda a cewarsa ba za’a lamunta da shi ba”.

Ya ce hadin gwiwar soja da tsaro da Iran ke yi da sauran kasashen duniya abu ne na doka da nufin kare muradun kasar da tsaron kasa.

Jami’in diflomasiyyar na Iran shawarci kungiyar EU da cewa kada ta fada cikin tarkon masu adawa da Iran, musamman gwamnatin wariyar launin fata ta sahyoniyawan, sannan kuma kada ta sadaukar da muradunta da dadaddiyar dangantakarta da Iran, saboda mutane da jam’iyyun da ke son kawo cikas ga Iran.”

Jami’an Iran sun bayyana cewa, kasar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen karfafa karfin sojinta ba, da kuma dakile ayyukanta da suka hada da na makami masu linzami.

Iran dai na mai nanata cewa ba wani makami mai linzami da ba Rasha domin yaki da Ukraine, kuma har kulum tana fifita hanyar diflomatsiyya domin warware rikicin na Rasha da Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments