MDD Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Bayan Harin Isra’ila A Arewacin Lebanon

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma cikakke cikin sauri bayan wani harin da Isra’ila ta kai kan wani

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma cikakke cikin sauri bayan wani harin da Isra’ila ta kai kan wani gini da ke arewacin Lebanon, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22 da suka hada da mata 12 da yara 2.

Wannan dai ya sanya adadin wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila kan Lebanon Hizbullah ya haura 2,300.

Kafin hakan dama MDD ta ce ta damu da ci gaba da kai hare hare da ake yi a iyakar wucin gadi tsakanin Lebanon da Isra’ila, inda sakatare janar na majalisar Antonio Guterres ya yi Allah wadai da asarar rayukan fararen hula da hare haren ke haifarwa.

Yayin wani taron manema labarai, kakakin sakatare janar din Stephane Dujarric ya ce luguden wuta a Aitou dake yankin arewacin Lebanon, ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 23, yana mai bayyana hakan a matsayin abun damuwa ainun.

Ya kara da cewa, MDD ta damu da tasirin hakan ga fararen hula dake bangarorin biyu, musamman na Lebanon, yana mai kira ga masu ruwa da tsaki da su girmama hakkin dake wuyansu karkashin dokokin kasa da kasa, ciki har da dokar jin kai ta kasa da kasa da ta kare fararen hula.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar (OCHA), ta ruwaito cewa, rikicin na ci gaba da raba mutane da matsugunansu, kuma hukumomi a Lebanon sun ce batun ya shafi mutane miliyan 1.2. Zuwa ranar 13 ga watan Oktoba nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments