Iran Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Harin Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Asibitin Shahidan Al-Aqsa

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan asibitin shahidan Al-Aqsa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan asibitin shahidan Al-Aqsa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan harin da ‘yan sahayoniya suka kai kan asibitin shahidan Al-Aqsa da ke tsakiyar Zirin Gaza, tare da daukar harin a matsayin misali karara na laifukan yaki.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Baqa’i ya yi Allah wadai da mummunan aika-aikar da yahudawan sahayoniyya suka aikata na kai harin wuce gona da iri  kan asibin shahidan Al-Aqsa da ke tsakiyar Zirin Gaza da muggan bama-bamai, wadanda suka haddasa tashin mummunar gobara tare da janyo shahadan Falasdinawa da jikkata wasu masu yaw ana daban. Kuma harin misali ne na aikata laifukan yaki da kuma wani bangare na shirin kisan gilla ga Falasdinawa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana haramcin kai hare-hare a wuraren taruwan fararen hula, musamman asibitoci da cibiyoyin motocin daukar marasa lafiya kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada, kuma ya yi la’akari da cewa hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai da gangan ne kan asibitoci da nufin kashe marasa lafiya da wadanda suka jikkata gami da likitoci da ma’aikata a cibiyoyin kiwon lafiya, duk wadanda muggan laifuka sun isa dalilin gurfanar shugabannin ‘yan mamaya a gaban kotun kasa da kasa kan aikata laifukan yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments