Mataimakin Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah Ya Ce Sun Farfado Daga Juyayi

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Hizbullahi ta farfado daga juyayinta kuma ta amince da sabon daidaito da ya faru

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Hizbullahi ta farfado daga juyayinta kuma ta amince da sabon daidaito da ya faru

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya bayyana cewa: Kungiyar Hizbullahi tana nan da karfinta duk kuwa da munanan raunukan da suka same ta, kuma ta dawo da lafiya da karfinta, yana mai jaddada cewa kungiyar ta gudanar da shawarwari ne na tsawon mako guda da ya gabata don aiwatar da wani sabon daidaiton da za a yi, kuma zai ci gaba  wanda zai dandana kuda ga abokan gaba.

Sheikh Na’im Qassim ya kara da cewa: – A cikin jawabinsa na uku tun bayan kisan da aka yi wa babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah – cewa: Makamai masu linzamin da ‘yan gwagwarmaya suka harba kan birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila sun tarwatsa filin jirgin sama na Ben Gurion, tare da kora yahudawan sahayoniyya miliyan biyu zuwa mafakan karkashin rami.

Sheikh ya kuma yi nuni da cewa: Kungiyar ta Hizbullahi za ta iya kai hari kan duk wani wuri a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma za ta zabi wurin da ya dace. Sannan ya jaddada cewa: Abin da ‘yan gwagwarmaya suka cimma a fagen daga a cikin makonni biyu da suka gabata, ya fi yadda ake zato, kuma babban aikin ‘yan gwagwarmaya shi ne kai farmaki kan makiya a duk inda suka shiga domin buya.

Har ila yau, Sheikh Qassim ya kuma aike da sako zuwa ga mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai jaddada cewa: Mafita ita ce tsagaita bude wuta, ya kuma kara da cewa, Yana mai ce wa yahudawan sahayoniyya kada ku yarda da abin da jami’anku suka shelanta, ku dubi yawan ‘yan uwanku da suka halaka a yakin da ake yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments