Falasdinawa 23 Ne Su Ka Yi Shahada A Daren Jiya

Rahotannin da suke fitowa daga Falasdinu sun ambaci cewa, HKI ta kashe Falasdinawa da su ka hada kananan yara da mata 23,a kudanci da tsakiyar

Rahotannin da suke fitowa daga Falasdinu sun ambaci cewa, HKI ta kashe Falasdinawa da su ka hada kananan yara da mata 23,a kudanci da tsakiyar Gaza.

Kamfanin dillancin Labarun “Anatoly” na kasar Turkiya ya ambaci cewa; Jiragen yakin HKI sun kai hari akan gidan “Abu “Du’aimah” a  garin Bani Suhaila dake gabashin garin Khan-Yunus, a kudancin zirin Gaza.

Majiyar ta ce, iyalan gida daya da su ka hada mata da kananan yara 10 ne su ka yi shahada sanadiyyar harin.

A garin Fakhari da yake a gabashin Khan-Yunus ‘yan sahayoniyar sun kai wani harin akan wani gida tare da kashe Falasdinawa 8, su ma mata da kananan yara.

An sami Karin wasu shahidai Falasdinawa 5 a tsakiyar  yankin Gaza yayin da wasu da dama su ka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments