Wani  Dan Sandan HKI Daya Ya Halaka A Kudancin Falasdinu

Kafafen watsa laabrun HKI sun bayar da labarin cewa daya daga cikin jami’ansu ya halaka sanadiyar bude masa wuta da aka yi a yankin Usdud

Kafafen watsa laabrun HKI sun bayar da labarin cewa daya daga cikin jami’ansu ya halaka sanadiyar bude masa wuta da aka yi a yankin Usdud dake kudancin Falasdinu.

Rahotannin sun ambaci cewa, a yau Talata ne wani Bafalasdine ya bude wuta akan sojojin HKI da suke a yankin Nir-Jalim, sannan ya matsa yankin “Mafraq-Yafni” a Usdud, ya bude wuta akan wasu ‘yan sanda.

‘Yan sandan na HKI sun aike da Karin wasu jami’an nasu zuwa yankin da aka kai harin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments