HKI Ta Bada Sanarwan Cewa Makaman Kunan Bakin Wake, Na Hizbullah Suna Bacewa Daga Na’urorin Rada

A sakamakon bincike na farko wanda sojojin HKI suka fitar bayan hare hare mafi muni wadanda kungiyar hizbullah ta kaiwa barikin sojoji na Binyamina da

A sakamakon bincike na farko wanda sojojin HKI suka fitar bayan hare hare mafi muni wadanda kungiyar hizbullah ta kaiwa barikin sojoji na Binyamina da ke kudancin birnin Haifa na HKI a ranar Lahadin da ta gabata, ya nuna cewa sojoji da dama sun halaka da kuma jikata wasu sojoji fiye da 70, tace na’urorin rada na sojojin HKI sun gano makaman daga nesa, amma kafin su fada kan bararsu sai suka bace daga na’urorin.

Hare haren kungiyar Hizbullah na ranar Lahadin da ta gabata dai, suna daga cikin hare hare mafi muni wadanda Hizbullah ta kaiwa sojojin yahudawan tun bayan fara yakin tufanul Aska a shekara ta 2023.

Akalla sojojin 4 ne aka tabbatar da halakarsu sannan wasu 58 suka ji Rauni. Amma wasu kafafen yada labaran HKI sun bayyana cewa sojojin da hare haren suka jikata ko suka halaka ya fi wannan adadin sosai.

Rahoton yahudawan sun bayyana cewa na’urorin rada sun gano makaman har suka fara Shirin kakkaboshi, sai ya bace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments