Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa samuwar sojojin kasashen waje a kasashen yankin baya taimakawa kasashen. Shugaban ya kara da cewa Iran tana son ganin ko wace kasa a yankin tana da cikekken yenta.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Pezeshkian yana fadar haka a jiya Litinin a lokacinda yake ganawa da mataimakin firai ministan kasar Azarbaijan Shahin Mustafayev, wanda yake ziyarar aiki a nan birnin Tehran.
Shugaban ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta fadada dangantaka tsakanin dukkan kasashen musulmi musamman makobta.
Ya ce: bama bukatar gina tatanga a kan iyakokin kasashemmu don tabbatar da tsaro. Kasashen yankin su bude kan iyakokinsu don harkokinka suwanci da zirga zirgan mutane. Ya ce yana bukatar a shimfiya layin dogo da kuma babbar hanya ta motoci tsakanin Iran da Azarbaijan
A nashi bangaren mataimakin firai ministan kasar Azarbaijan yace kasarsa tana bukatar fadada dangantaka da kasar Iran a fagagen kasuwanci, tattalin arziki tsaro da sauransu.