Babban Sakataren MDD Yace Mai Yuwa Hare Haren Da HKI Ta Kaiwa Rundunar UNIFIL A Kudancin Lebanon Ya Zama Laifin Yaki

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa mai yuwa hare haren da sojojin HKI suka kaiwa rundunar tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar a kasar

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa mai yuwa hare haren da sojojin HKI suka kaiwa rundunar tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar a kasar Lebanon UNIFIL ya zama laifin yaki.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto babban sakataren yana fadar haka bayan da ya sami rahoton cewa wasu dakarun UNIFIL da suke aikin tabbatar da zaman lafiya a kudancin kasar Lebanon sun ji rauni saboda barin wutan da sojojin HKI suka yi masu a cikin yan kwanakin da sukagabata.

Kafin haka dai a ranar Lahadin da ta gabata ce mai magana da yawun babban sakataren ya ce kai hari kan sojojin MDD laifin yaki ne, kuma yakamata a gudanar da bincike kan abinda ya faru a kudancin kasar Lebanon.

Kasashen 40 ne dai suka yi karo-karo don hada dakarun UNIFIL a kudancin kasar Lebanon, kuma dukkan kasashen sun nuna goyon bayansu ga dakarun, sannan sun yi allawadai da sojojin HKI wadanda suka kai masu hare hare a kan cibiyar su da ke garin Naqura a kudancin kasar Lebanon, inda sojoji 5 daga cikinsu suka ji rauni.

Frai ministan HKI Benyamin Natanyaho ya bukaci MDD ta janye dakarun UNIFIL daga kudancin kasar Lebanon, don a halin yanzu sun zama garkuwa ga mayakan Hizbullah  a fadinsa.

Kasashe da dama a duniya da kuma kungiyar Tarayyar Turai sun yi allawadai da HKI a hare haren da sojojinta suka kai kan dakarun na Unifil.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments