Iran : Yaki Ko Zaman Lafiya, Duk A Shirye Muke Mu_Araghchi

Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa bata son yaki amma kuma a shirye ta ke ta kare hurimin kasarta. ”Muna shirye

Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa bata son yaki amma kuma a shirye ta ke ta kare hurimin kasarta.

”Muna shirye idan yaki ne, haka ma a shirye mu ke idan zaman lafiya ake so” Inji Ministan harkokin wajen aksar ta Iran Seyyed Abass Araghchi.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a binrin Bagadaza bayan ganawarsa da ministan harkokin wajen Iraki.

A nasa bangare ministan harkokin wajen Iraki, Fouad Hussein, ya bayyana cewa Iraki ba zata lamunta a yi amfani da sararin samaniyarta ba wajen kai hari kan Iran.

Araghchi Ya isa babban birnin kasar Iraki ne a wani bangare na rangadin da ya kai a kasashen Lebanon, Siriya da Saudiyya a kokarin samar da zaman lafiya mai adalci a Gaza da Lebanon.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments