Pezeshkian Da Macron, Sun Tattauna Kan Halin Ake Ciki A Yankin

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron sun tattauna ta wayar tarho kan hanyoyin kawo karshen rikici a yankin da kuma

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron sun tattauna ta wayar tarho kan hanyoyin kawo karshen rikici a yankin da kuma samar da tsagaita wuta a Lebanon.

Shugabannin kasashen biyu sun tattauna kan sabbin abubuwan da ke faruwa a yankin musamman yadda rikicin kudancin kasar Labanon ke kara ruruwa.

A yayin wannan zantawar, shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ko da yaushe tana son samar da wani yanki mai tsaro, nesa da yaki da tashe-tashen hankula, kuma tana maraba da tsagaita bude wuta da dakatar da yaki da kuma rikici:

Ya kara da cewa, Iran ta kai zuciya nesa bayan kisan da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran a farkon watan Yuli, inda ta fifita bada damar diflomasiyya ga kasashen yammacin duniya ta cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.

“Duk da haka, a cewar Pezeshkian yahudawan sahyoniya sun matsa kaimi wajen keta dukkan dokokin kasa da kasa ta hanyar kara kai hare-haren bama-bamai da aikata laifuka a Gaza da yada rikicin zuwa Lebanon,” in ji.

Shugaban ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi maraba da goyon bayan duk wata shawara da za ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, shugaban ya kuma yi kira ga takwaransa na Faransa da ya hada kai da sauran kasashen Turai wajen tilasta wa Isra’ila kawo karshen kisan kiyashi da laifukan da ke ci gaba da faruwa a Zirin Gaza da Lebanon.

Massaoud Pezeshkian ya kuma yi marhabin da matsayin gwamnatin Faransa na baya-bayan nan na yin Allah wadai da ayyukan gwamnatin Isra’ila a Lebanon da kuma yanke shawarar kawo karshen isar da makamai ga gwamnatin Isra’ila da aka yi niyya don yakin Gaza.

A nasa bangaren shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga takwaran nasa na Iran da yayi amfani da tasirin kasarsa wajen kwantar da hankula a zirin Gaza da Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments