Rikicin Sudan Ya Yi Ajalin Rayukan Mutum 30 A Cikin Kwanaki Biyu

Rahotanni daga Sudan an cewa mutane sama da talatin ne suka rasa rayukansu kana wasu da dama suka jikkata a ci gaba da yakin da

Rahotanni daga Sudan an cewa mutane sama da talatin ne suka rasa rayukansu kana wasu da dama suka jikkata a ci gaba da yakin da ake yi tsakanin sojojin Janar Abdel Fattah Al Burhane da na Janar Mohamed Hamdane Daglo.

Bayan harin bam da aka kai a wani masallaci a ranar Juma’a 11 ga watan Oktoba a sansanin ‘yan gudun hijira na Abou Chouk da ke kusa da El-Fasher, an kai wani hari kan wata kasuwa a birnin Khartoum, babban birnin kasar, a ranar 12 ga watan Oktoba.

Wata hadakar kungiyar masu sa-kai don aikin ceto a Sudan ta ce sojojin Sudan sun kai hari ta sama kan kasuwar a birnin Khartoum, inda suka kashe mutane 23.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, yakin na sama da watanni 16 a Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 20,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments