Hizbullah Ta Lebanon Ta Kai Hari Kan Birnin Haifa Tare Da Kashe Yahudawan Sahayoniyya

‘Yan gwagwarmayar Hizbullahi sun kai wani mummunan hari kan birnin Haifa na haramtacciyar kasar Isra’ila dazu-dazun nan Rundunar sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar

‘Yan gwagwarmayar Hizbullahi sun kai wani mummunan hari kan birnin Haifa na haramtacciyar kasar Isra’ila dazu-dazun nan

Rundunar sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da cewa: Wasu hare-hare da ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon suka kai da jirgin sama maras matuki ciki kan yankin Benyamin da ke birnin Haifa na haramtacciyar kasar kasar Isra’ila ya halaka yahudawa sahayoniyya masu yawa tare da jikkata wasu 39 na daban.

Kafofin yada labaran yahudawan sahayoniyya sun bayanna cewa: Bayan harin jirgin saman maras matuki ciki, ‘yan gwagwarmayar Hizbullahi sun kuma harba makami mai linzami kan wajen da jirgin saman ya yi barna lamarin da ya janyo fashe-fashe a yankin.

Kamar yadda kungiyar ta Hizbullahta sanar da karin kai hari kan yankin Tuddan Jolan da aka mamaye, kuma harin ya cimma yahudawan sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments