Jaridar Haaretz Ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ta Ce`Ana Jiran Lokacin Rugujewar Isra’ila

Jaridar Ha’aretz ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce: Tana tsammanin ƙarshen jini, hawaye da rugujewa haramtacciyar kasar Isra’ila Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Ha’aretz tana

Jaridar Ha’aretz ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce: Tana tsammanin ƙarshen jini, hawaye da rugujewa haramtacciyar kasar Isra’ila

Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Ha’aretz tana tsammanin zuwan lokacin kawo ƙarshen zubar da jini da hawaye da kuma tabbataccen lokacin rugujewar gwamnatin ‘yan sahayoniyya.

Jaridar Ha’aretz ta rubuta cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana rayuwa ce cikin girman kai kuma tana son sauya tsarin yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan girman kai ya sanya ta tana rayuwa cikin tsammanin yaudaruwar samun nasara lamarin da babu makawa za ta kare cikin zuban jini da hawaye da kuma rugujewa da daidaicewa.

Wakilin tashar Al-Alam a Ramallah ya ce: Ha’aretz jarida ce mai ra’ayin hagu, wacce ake daukarta daya daga cikin tsoffin jaridun yahudawa, ba ta rubuta labarinta a kan motsin rai, a’a tana rubuta su ne bisa hujja.

Wakilin Al-Alam ya yi ishara da labarin da tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila da ke tabbatar da cewa: Jiragen sama masu saukar ungulu na haramtacciyar kasar Isra’ila suna tafiye-tafiye a tsakanin kudancin Lebanon da asibitin Rambam da ke Haifa domin jigilar wadanda suka jikkata daga fadace-fadacen kudancin Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments