An Sanar Da Lokacin Yin Jana’izar Janar Shahid Nilofurushan

Kamfanin Dillancin labarun Irna ya nakalto cewa, za a yi jana’izar janar shahid Nilofurushan  a Jibi Talata da misalin karfe 9 na safe daga filin

Kamfanin Dillancin labarun Irna ya nakalto cewa, za a yi jana’izar janar shahid Nilofurushan  a Jibi Talata da misalin karfe 9 na safe daga filin Imam Husain zuwa Filin Shahidai dake nan Tehran.

Gabanin kawo jikin shahidin, za a kai shi  biranen Najaf, hubbaren Imam Ali ( a.s) sai kuma Karbala, wurin Imam Husain, sannan wurin Imam Ridha ( a.) a garin Mashad.

Idan an yi jana’izarsa a nan Tehran a ranar Talata, za a kai shi garin Isfahan a ranar Alhamis, inda za a binne shi.

Sanarwar yadda za a gudanar da jana’izar shahid Abbas Nilofurashan ta fito ne daga dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran a yau Lahadi.

Shi dai Abbas Nilofurushan ya yi shahada ne a ranar Juma’a 27 ga watan Satumba tare da sayyid Hassan Nasrallah na kungiyar Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments