Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Cilla Makamai Masu Linzami  Kan Birnin Tel Aviv Babban Birnin HKI

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwar kai hare hare tare da amfani jirgen yaki masu kunan bakin wake, wato ‘Drones’ kan birnin Tel

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwar kai hare hare tare da amfani jirgen yaki masu kunan bakin wake, wato ‘Drones’ kan birnin Tel Aviv  babban birnin Yahudawan sahyoniyya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kungiyar na Fadar haka a jiya Asabar da yamma. Ta kuma kara da cewa dakarun na Hizbulla sun yi amfani da makaman ‘Drones’ na kunan bakin wake samfurin Kamikaze don aiwatar da wadan nan hare hare.

Labarin ya kara da cewa kungiyar Hizbullah ta kai wadan nan hare hare ne saboda maida martani kan hare haren da sojojin HKI suke kaiwa kan fararen hulla a cikin kasar Lebanon da kuma kan Falasdinawa a Gaza..

Kungiyar ta shiga yaki da HKI ne a ranar 8 ga watan Octoban shekara ta 2023 don tallafawa Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke kashewa a Gaza. Kuma a cikin shekara guda da ta gabata, sun kashe Falasdinawa fiye da 41,000 mafi yawansu mata da yara. A kasar Lebanon kuma sun kashe mutane kimani 2000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments