Gwamnatin Biden ta amince da sayar da makamai na biliyoyin daloli ga Saudiyya da UAE

Gwamnatin Biden ta amince da sayar da makamai na biliyoyin daloli ga Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, biyu daga cikin manyan kawayenta a yankin gabas

Gwamnatin Biden ta amince da sayar da makamai na biliyoyin daloli ga Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, biyu daga cikin manyan kawayenta a yankin gabas ta tsakiya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da Majalisar dokokin kasar cewa ta amince da sayar da makamai masu linzami na Hellfire da Sidewinder, da kuma makaman atilare, da tankokin yaki, da kuma bindigogi ga Saudiyya, inda yarjejeniyar ta haura dala biliyan daya.

A cikin watan Agusta, Shugaba Joe Biden ya cire takunkumi kan siyar da makamai ga Saudiyya. Tun bayan kaddamar da farmakin guguwar Al-Aqsa a ranar 7 ga Oktoba, 2023, Sojojin Yaman suka zafafa kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila a cikin tekun Bahar Maliya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen ta kuma sanar da ‘yan majalisa game da amincewarta na yiwuwar siyar da tsarin roka na GMLRS, makamai masu linzami masu cin dogon zango na ATACMS, da horo da tallafi ga Hadaddiyar Daular Larabawa, da zasu lakume kudi har dala biliyan 1.2.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments