Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta dauki alhakin kai sabbin hare-hare da makami mai linzami kan birnin Haifa, na Isra’ila.
Bayan amfani da jirage marasa matuka masu fashewa wajen kai hari a wani sansanin sojin sama, kungiyar ta sanar da cewa ta harba “makamaimai” kan wani sansanin soji da sanyin safiyar yau Asabar.
Ana ci gaba da samun karuwar tashe-tashe hankula sakamakon farmakin da Isra’ila ke kaiwa kasar ta Lebanon.
A wani labarin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, sama da mutum 420,000 ne suka tsallaka zuwa Syria daga Lebanon tun farkon hare-haren Isra’ila.
Sama da ‘yan kasar Syria 310,000 da ‘yan kasar Lebanon 110,000 ne suka tsallaka zuwa Syria a ranar 23 ga watan Satumba zuwa 9 ga watan Oktoba, in ji mai magana da yawun ofishin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, a wani taron manema labarai a Geneva.