Gwamnatin Nicaragua ta sanar da katse huldar diflomasiyya da Isra’ila wacce ta kwashe shekara guda tana yakin kisan kare dangi kan al’ummar Falasdinu a zirin Gaza.
Mataimakin shugaban kasar Nicaragua Rosario Murillo ne ya sanar da daukar matakin ga kafafen yada labaran kasar a ranar Juma’a.
Rikicin, in ji gwamnatin Nicaragua, yanzu haka kuma “ya kara tsananta kan Lebanon kuma yana matukar barazana ga Syria, Yemen da Iran.”
Isra’ila ta kaddamar da yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba bayan da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta kaddamar da harin ba zata kan ‘yan mamaya a matsayin mayar da martani ga kazamin cin zarafi da Isra’ila ke yi kan Falasdinawa a yammacin gabar kogin Jordan.
Hare-haren da gwamnatin kasar ta kai a zirin Gaza ya zuwa yanzu ya kashe akalla Falasdinawa 42,150 tare da jikkata wasu 98,117.
Shugaban Colombia Gustavo Petro ya yanke huldar diflomasiyya da Isra’ila a watan Mayu, yana mai kiran gwamnatin firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da “kisan kare dangi”.
Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva shi ma ya kira jakadan kasar a yankunan da aka mamaye a wannan watan.