Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Muhimmancin Alaka Da Kasar Rasha

Shugaba Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gana da takwaransa na Rasha a bayan fagen taron da ake yi a kasar Turkmenistan dangane da al’adu da cigaban

Shugaba Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gana da takwaransa na Rasha a bayan fagen taron da ake yi a kasar Turkmenistan dangane da al’adu da cigaban al’ummu, ya kara da cewa; Tattalin arzikin kasashen biyu da kuma al’adunsu suna kara damfaruwa da juwa da karfi  a kowace rana.

Shugaba Fizishkiyan ya kuma ce; Kasashen biyu suna da damammakin da za su iya amfanuwa da su, da kuma suke bukatuwa da juna.

Da yake Magana akan halin da ake ciki a wannan yakin na yammacin Asiya, shugaban na kasar Iran ya yi suka da kakkausan murya akan yadda HKI take take dukkanin dokokin kasa da kasa da hakkin bil’adama. Bugu da kari ya zargi kasashen turai da Amurka saboda yadda suke goyon bayan HKI da kuma kin amincewarsu da zaman lafiya a cikin wannan yankin.

A nashi gefen, shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya gayyaci shugaban na kasar Iran zuwa halartar taron kungiyar BRICS, tare kuma da cewa za su yi ganawar a yayin taron.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments