An Gano Gawar  Janar Nilofurushan Da Ya Yi Shahida A Lebanon

A jiya Juma’a ne aka sanar da gano gawar Manjo Janar Abbas Nilforushan a birnin Beirut, wanda ya yi shahda ne a tare da Sayyid

A jiya Juma’a ne aka sanar da gano gawar Manjo Janar Abbas Nilforushan a birnin Beirut, wanda ya yi shahda ne a tare da Sayyid Hassan Nasrallah a wani mummuna harin da jiragen yakin HKI su ka kai a unguwar “Dhadiya” a ranar 27 ga watan Satumba.

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ne su ka sanar da gano gawar janar shahidin, wanda su ka bayyana shi a matsayin daya daga cikin gwarazan gwgawarmaya.

Sanarwar da dakarun kare juyin musuluncin su ka fitar, sun mika sakon ta’aziyya ga iyalan shahidin, da ‘yan’uwansa ‘yan gwagwarmaya,tare da bayyana cewa, ayyukan da ya yi za su cigaba.

Sai a nan gaba ne za a sanar da lokacin da za a yi masa jana’iza a nan Iran.

A ranar Juma’a ta 27 ga watan Satumba ne dai Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu da goyon bayan Amurka ya bayar da umarnin kashe Sayyid Hassan Nasrallah, babban magatakardar kungiyar Hizbullah.

Jiragen saman HKI Sun harba makamai masu linzami masu yawa da nauyin bama-baman da su ka sauka akan gine-ginen Dhahiya sun kai ton 85.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments