Jirgi Maras Matuki Daga Lebanon Ya Yanke Wutar Lantarki A Wani Sashe Na Birnin Tel Aviv

A jiya juma’a da dare, mayakan Hizbullah sun harba wasu jirage marasa matuki da  su ka ci nisan kilo mita 100 ba tare da makaman

A jiya juma’a da dare, mayakan Hizbullah sun harba wasu jirage marasa matuki da  su ka ci nisan kilo mita 100 ba tare da makaman HKI sun kakkabo su ba,  daya ya fada a yankin Herzliya dake kudancin birnin Tel Aviv, tare da yanke wutar lantarki a cikinsa.

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, an ji karar jiniyar gargadi a lokacin da jiragen biyu marasa matuki su ka isa samaniyar birnin na Herzliya, bayan da aka iya kakkabo daya, daya kuma ya fada akan wani gini tare da daukewar wutar lantarki.

Tuni magajin garin na Herzliya ya kira yi mazaunansa da su kasance a kusa da dakunan buya na karkashin kasa.

Ma’aikatan kashe gobara sun ce, an sami afkuwar asar a a cikin wurare daban-daban na cikin yankin.

 Tashar talabijin din ‘almayadeen’ ta ce, wannan shi ne zango mafi nisa da wani makami da aka harba daga Lebanon ya ci, tun farkon yaki.

.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments