Iraki ta yi Allah wadai da cin zarafin Ayatollah Sistani da kafafen yada labaran Isra’ila suka yi

Gwamnatin Iraki ta yi Allah wadai da matakin da kafafen yada labarai na gwamnatin sahyoniyawan suke yi na cin mutuncin babban malamin addini na kasar

Gwamnatin Iraki ta yi Allah wadai da matakin da kafafen yada labarai na gwamnatin sahyoniyawan suke yi na cin mutuncin babban malamin addini na kasar Iraki.

Kafafen yada labaran kasar Iraki sun bayyana cewa, kakakin gwamnatin Irakin ya yi Allah wadai da laifukan da gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya ta yi kan al’ummar Gaza da Labanon da kuma ayyukan wariya na wannan gwamnati, yana mai cewa kasar Iraki tana matukar adawa da duk wani cin fuska ga matsayin malamai.

A ranar Larabar da ta gabata ne ofishin firaministan kasar Iraki ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ambato Bassem Al-Awadi kakakin gwamnatin kasar Irakin yana cewa, bayan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta shiga cikin kisan kiyashi da munanan laifuka na cin zarafin bil’adama da kisan kai da fyade da ake yi wa al’ummar Gaza da Labanon, kafofin yada labarai na masu wadannan masu tayar da hankali da nuna wariya suna cin mutuncin matsayi na addini.

Al-Awadi ya kara da cewa gwamnatin kasar Iraki tana matukar adawa da duk wani batanci ga wannan mukami, wanda dukkanin al’ummar Iraki, kasashen Larabawa, Musulunci, da sauran kasashen duniya suke girmamawa da mutuntawa.

Wannan jami’in na Iraki ya ce kasarsa ta yi gargadin hadarin da ke tattare da wadannan yunkuri bisa tushen wariya da kuma dagewa kan cin mutuncin manyan mutane masu girma a cikin al’ummomi, wanda ke haifar da yanayin da zai kara barazana ga tsaro da zaman lafiya na duniya.

Kakakin gwamnatin Irakin ya yi nuni da cewa, gwamnatin sahyoniyawan ta sake tabbatar da cewa, gungun masu laifi ne kawai da ke yin rayuwa ta hanyar haifar da rikice-rikice, wuce gona da iri da yaki, tare da kara jefa duniya cikin bala’oi.

Kakakin gwamnatin Iraki ya yi kira ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen duniya da su yi Allah wadai da duk wani aiki na cin mutuncin musulmin duniya da yunkurin cin mutuncin masu fada aji a cikin al’ummomi a matakin kasa da kasa.

A ranar Talata kafafen yada labaran yahudawan sun buga hotunan Ayatullah al-Sistani babban malamain addini a kasar Iraki a matsayin daya daga cikin wadanda gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila za ta yi wa kisan gilla.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments