Haifa:“Yan Share Wuri Zauna Biyu Sun Halaka A Harin Hizbullah

Rahotannin da suke fitowa daga HKI sun ce ‘yan share wuri zauna  biyu sun halaka sanadiyyar harin makamai masu linzami da dakarun Hizbullah na Lebanon

Rahotannin da suke fitowa daga HKI sun ce ‘yan share wuri zauna  biyu sun halaka sanadiyyar harin makamai masu linzami da dakarun Hizbullah na Lebanon su ka kai akan garin Haifa a yau Laraba.

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, makamai masu linzamin da aka harbo daga Lebanon sun fada kan garin ne, bagatatan ba tare da jiniyar gargadi ta kada ba, ko kuma makaman da ake da su sun iya kakkabo su.                                                                                                                                                                                                          

Bugu da kari, gobara ta tashi a wurare mabanbanta a cikin sansanin ‘yan share wuri zauna na “Kirayot-Shimona” sanadiyyar saukar makamai masu linzami daga Lebanon.

A filin dagar yakin kasa kuwa, Hizbullah ta sanar da cewa, ta tashi nakiya a tsakanin sojojin mamayar HKI da suka yi kokarin shiga cikin garin Balida, sannan kuma su ka yi fada gaba-da gaba da su, da tare da kashe da dama daga cikinsu da kuma jikkata wasu.

A yankin Labbuna ma sojojin mamayar sun yi kokarin kutse amma hare-haren dakarun Hizbullah ya tilasta musu janyewa da komawa inda su ka fito.

A Maisul-Jabal ma dai mayakan na Hizbullah sun kashe tare da jikkata sojojin mamaya masu yawa ta hanyar harba musu makamai masu linzami.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments