An Jikkata “Yan Share Wuri Zauna Da Dama A Garin Khudairah Dake Arewacin Tel Aviv

Rahotanni daga HKI sun ce mutane 6 ne su ka jikkata, 5 daga cikinsu suna cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai,sanadiyyar sukarsu da wuka da

Rahotanni daga HKI sun ce mutane 6 ne su ka jikkata, 5 daga cikinsu suna cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai,sanadiyyar sukarsu da wuka da wani Bafalasdine ya yi.

Kungiyar leken asirin cikin gida a HKI “Shabak” da kuma ta agaji “ Dadiv Star” sun isa wurin da lamarin ya faru, domin gudanar da bincike da kuma daukar wadanda aka raunata zuwa asibiti.

Jaridar “Yisa’il Home” ta ce, wanda ya yi sukar da wukar sunanshi Ahmad Jabarin dan shekaru 36, kuma ya fito ne daga garin Ummu-Faham.

Majiyar ta ce tuni an kashe maharin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments