Jirgin Saman “Turkish Airline” Ya Yi Saukar Gaggawa Saboda Mutuwar Daya Daga CIkin Matukinsa A Sararin Samaniya

Kamfanin jirgin sama na “ Turkinsh AirLine” wanda mallakin gwamnatin Turkiya ne, ya sanar da cewa, daya daga cikin matukan jiragensa ya rasu a daidai

Kamfanin jirgin sama na “ Turkinsh AirLine” wanda mallakin gwamnatin Turkiya ne, ya sanar da cewa, daya daga cikin matukan jiragensa ya rasu a daidai lokacin da jirgin yake tafiya a sararin samaniya, daga birnin Seattle  na kasar Amurka, zuwa birnin Stanbul na Turkiya, lamarin da ya tilasa yin saukar gaggawa a birnin New-York.

Lamarin ya faru ne jim kadan bayan da jirgin ya taso daga Seattle  da  marecen yau Laraba,daya daga cikin matukansa ya sume, kuma duk kokarin da aka yi na ba shi taimakon gaggawa bai yi amfani ne, domin a karshe ya ce ga garinku.

Kakakin kamfanin na “Turkish Airline” Yahya Ustun ne ya  wallafa wannan sanarwar a shafinsa na sada zumunta. Mamacin dai ya fara aiki ne da kamfanin tun a 2007, kuma a cikin watan Maris na wannan shekara an yi masa wasu gwaje-gwaje na lafiya da hakan yake nuni da cewa, yana fama da wani ciwo, wanda ba a bayyana shi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments